Nazarin Kundin Tsarin Mulki: Majalisun ƙasar nan sun amince da ƙirƙirar sababbin jihohi shida a Najeriya
Kwamitin haɗin gwiwa na majalisar dattawa da ta wakilai kan sake duba kundin tsarin mulki ya amince da ƙirƙirar sababbin jihohi shida a ƙasar.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa, wannan matsaya ta fito ne daga taron kwana biyu da aka gudanar a Legas ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, da mataimakin kakakin majalisar wakilai, Benjamin Kalu.
Kwamitin ya duba jimillar kudurori 69, ciki har da buƙatun ƙirƙirar jihohi 55, sake fasalin iyakoki biyu, da ƙirƙirar ƙananan hukumomi 278.
Bayan nazari, kwamitin ya amince da ƙara jiha ɗaya a kowanne yanki na siyasa guda shida, wanda idan an tabbatar da shi zai ƙara adadin jihohi daga 36 zuwa 42.
A sabon rabe-rabe, kudu maso kudu da kudu maso yamma za su zama da jihohi bakwai-bakwai, kudu maso gabas da jihohi shida, arewa maso yamma da jihohi takwas, yayin da arewa maso gabas da arewa ta tsakiya za su kasance da jihohi bakwai-bakwai.
Haka kuma, an kafa wani ƙaramin kwamiti ƙarƙashin jagorancin Sanata Mohammed Tahir Monguno domin tantance yankunan da za a fitar da sababbin jihohin daga cikinsu tare da tabbatar da adalci ga dukkan masu neman ƙirƙirar jiha.












































