Hukumar Hisbah ta kama mutane 25 bisa zargin shirya auren jinsi a Kano

Kano Hisbah

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mutane 25 bisa zargin shirya auren jinsi a unguwar Hotoro da ke cikin birnin Kano.

Mataimakin kwamandan hukumar, Mujahedeen Aminudeen, ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da hukumar ta aikowa jaridar Solacebase a ranar Lahadi.

Ya bayyana cewa waɗanda aka kama sun haɗa da maza 18 da mata 7, inda jami’an hukumar suka cafke su a cibiyar taro ta Fatima Event Centre da ke kan hanyar Hotoro Bypass a ranar Asabar.

Aminudeen ya ce, hukumar ta samu sahihan bayanai cewa wasu suna shirin gudanar da auren jinsi, lamarin da ya sa jami’an hukumar suka isa wurin cikin gaggawa suka kuma kama mutane 25 da ake zargi da hannu a ciki.

Ya ƙara da cewa waɗanda aka kama sun fito daga yankuna daban-daban kamar Sheka, Yar Gaya da Kofar Nasarawa, tare da ƙarin bayani cewa hukumar ba za ta lamunci duk wani abu da zai ɓata tarbiyyar al’umma a Kano ba.

Aminudeen ya kuma yi kira ga jama’a da su taimaka wa hukumar Hisbah da bayanai kan ayyukan da ke sabawa tarbiyya a cikin jihar, yana mai jaddada cewa hukumar za ta ci gaba da tabbatar da ɗa’a da ladabi a cikin al’umma.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here