Hukumar kula da Gasa da haƙƙin masu amfani da kayayyaki ta ƙasa FCCPC ta sake nanata aniyarta na tabbatar da ciniki cikin gaskiya da kare masu amfani da kayayyaki a Kano da fadin ƙasar nan, domin tsaftace harkokin kasuwanci da hana mamaye kasuwa ta hanya ɗaya.
A yayin ziyarar ta zuwa ofishin hukumar na Kano, kwamishinar gudanarwa ta hukumar, Hajiya Ummusalma Isyaka Rabi’u, ta bayyana muhimmancin ciniki cikin gaskiya ga daidaiton tattalin arzikin ƙasa.
Ta ce, an kafa hukumar ne domin kare haƙƙin masu amfani da kayayyaki tare da tabbatar da kamfanoni suna gudanar da harkokinsu ba tare da mamaye kasuwa ba.
Hajiya Ummusalma ta bayyana cewa hukumar tana da doka mai ƙarfi da ke ba ta damar sa ido a kan kasuwanci da tabbatar da bin ƙa’idoji.
Ta ce a Kano an kafa kwamiti na musamman da zai dinga sa ido don tabbatar da cewa babu ɓarna a kasuwanci.
Karin labari: Gwamnan Kano ya rushe shugabancin hukumar kare hakkin masu saye ta jihar
Ta ƙara da cewa hukumar na haɗin gwiwa da ma’aikatar noma wajen tabbatar da gaskiya da adalci a harkokin noma da samar da abinci, tare da kare manoma da masu saye daga cin zarafi.
Hajiya Ummusalma ta kuma bayyana cewa hukumar ta fara amfani da kafafen sadarwa na zamani domin bai wa ‘yan ƙasa damar yin ƙorafi da samun kariya cikin sauƙi.
Ta jaddada cewa, kafa ofishin Kano ya nuna jajircewar hukumar wajen faɗaɗa ayyukanta a Arewa da tabbatar da cewa masu amfani da kayayyaki sun fi samun kariya daga cin zarafi.













































