Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da rushe shugabancin hukumar kare hakkin masu saye ta jihar Kano.
Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Umar Faruk Ibrahim, ne ya sanar da haka, inda ya bayyana cewa matakin ya zama dole saboda rikicin shugabanci da ya daɗe yana damun hukumar duk da yunkurin sulhu da gwamnati ta yi.
Sanarwar da sakataren ya fitar ta ce rushewar ta shafi shugaban hukumar, sakataren gudanarwa, da dukkan mambobi ciki har da wakilai na musamman.
Sanarwar ta umarci dukkan jami’an da abin ya shafa da su mika ragamar hukumar da duk kadarorin gwamnati da ke hannunsu ga babban jami’i mafi girma a hukumar kafin ƙarshen ranar Litinin, 27 ga Oktoba, 2025.
Takardun mika ragamar za a tura su zuwa ofishin sakataren gwamnatin jihar ta sashen bincike, kimantawa da harkokin siyasa, da kuma ofishin kwamishinan ma’aikatar zuba jari da kasuwanci.
Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa za ta ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatar da gaskiya, ingantaccen aiki, da kyakkyawan shugabanci a dukkan hukumominta.













































