Kwamitin binciken tashe-tashen hankulan siyasa da na mutanen da suka rasa rayukansu a jihar Kano, ya bayyana al’amuran da suka faru tun daga zabukan 2015 zuwa 2023, ta ba da tabbacin cewa za ta gurfanar da wadanda ke da hannu wajen tayar da rikicin siyasa a jihar.
Jaridar SolaceBase ta rawaito cewa shugabar hukumar mai shari’a Zuwaira Yusuf ta bayyana haka a yayin taron kaddamar da wata babbar kotun shari’a dake kan titin Miller a jihar Kano.
Karin labari: Da Dumi-Dumi: Kakakin majalisar Edo ya dakatar da ‘yan majalisa 3
Zuwaira ta jaddada cewa babbar manufar hukumar ita ce ta binciki tushe da kuma abubuwan da ke haifar da tashe-tashen hankulan siyasa a jihar, inda ta kara da cewa hukumar za ta gano takamaiman wuraren da tashe-tashen hankulan da suka shafi zabukan 2015 da 2019 da kuma 2023 suka faru a jihar Kano.
Haka kuma, hukumar za ta yi taka-tsan-tsan wajen zakulo wadanda aka samu tashe-tashen hankula daban-daban da suka hada da na siyasa da kuma ayyukan da gwamnati ta dauki nauyi. Bugu da kari, za ta binciki yawan mutanen da suka bata.
Karin labari: Najeriya za ta rage lantarkin da ta ke bai wa Nijar da Benin da Togo
Ta ci gaba da cewa, “Manufarmu ita ce mu saukaka tare da tabbatar da cewa an gurfanar da wadanda suka dauki nauyin tashe-tashen hankulan siyasa a lokacin zabukan 2015 da 2019 da kuma 2023, da sauran nau’ikan tashe-tashen hankula.”
Ta yi nuni da cewa aikin hukumar ya shafi bayar da shawarwarin dawwamammen mafita kan wadannan batutuwa. Don haka, ta gayyaci daidaikun mutane da kungiyoyi da na farar hula (CSOs) da kungiyoyi masu zaman kansu (NGOs), da wadanda abin ya shafa da ‘yan uwansu da su mika takarda ko koke ga Hukumar daga yau.
Karin labari: Da Dumi-Dumi: Gobara ta tashi a gidan tsohon Gwamnan Kano Ibrahim Shekarau
A cewarta, ya kamata a mika wadannan bayanan zuwa wurin rajistar Hukumar, da ke cikin harabar Kotun.
Mai shari’ar ta tabbatarwa da jama’a cewa Hukumar ta himmatu wajen yi musu hidima, tare da yin alkawarin yin nazari sosai kan koke-koke, tare da kiran mutane da su ba da shaida ta baki.
Ta nanata cewa Hukumar za ta gudanar da ayyukan da aka dora mata ba tare da nuna son kai ba, domin tabbatar da adalci ga al’ummar Jihar Kano.