Kano: Jami’an tsaro sun garkame inda aka shirya yin zanga-zanga

NUJ A 1
NUJ A 1

Hukumomin tsaro a jihar Kano sun garkame shalkwatar ‘yan jaridu ta jihar, inda aka shirya gudanar da zanga-zangar lumana dangane da matsalar tsaro da ake fama da ita a arewan Nigeria.

Tun da sanyin safiya Hukumomin tsaron hada da jami’an ‘yan sanda dana DSS da kuma Civil Defence suka mamaye wajen da motoci, inda suka hana kowa shiga.

Da yake zantawa da manema labarai daya daga cikin wanda suka shirya zanga-zangar Barrista Abba Hikima ya ce dalilin shirya zanga-zanga shine sun fito su nunawa gwamnatin rashin jin dadi dangane da abubuwan da suke faruwa ta fuskar rashin tsaro.

Ya ce kundin tsarin mulki ya bada da idan al’umma sun shugabanni suna yin ba daidai ba, su yi amfani da abinda doka ta tanadar domin janyo hankalin shugabanni kan su ringa gudanar da ayyukan su yadda ya kamata.

Ya kara da cewa kundin tsarin mulkin Nigeria bai ce idan za’a gudanar da zanga-zanga sai an sanar da jami’an tsaro ba.

Da yake nasa jawabin shugaban kungiyar ‘yan jaridu reshen jihar Kano Abbas Ibrahim ya ce basu san da zanga-zangar ba, kuma basu bawa kowa damar yin amfani da sakatariyar a matsayin wajen yin zanga-zanga ba.

Ya ce iya abinda suka sani shine Gamayyar kungiyoyin arewa sun sanar dasu cewa zasu gudanar da taron manema labarai, don haka basu da wata masaniya kan zana-zanga.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here