‘Yan bindiga sun hallaka dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Giwa a majalisar dokokin jihar Kaduna Rilwanu Aminu Gadagau a kan hanyar Kaduna zuwa Zaria.
Rahotanni sun bayyana cewa an hallaka dan majalisar ne a daren litinin din da ta gabata, lokacin da ‘yan bindiga suka kai wani hari, inda sai a safiyar yau laraba aka samu gawar dan majalisar a kan titin Kaduna zuwa Zaria.
Rilwanu Aminu Gadagau shine shugaban kwamitin kananan hukumomi da ci gaban karkara na majalisar dokokin jihar Kaduna.
Idan baku manta bam un kawo muku labarin yadda ‘yan bindiga suka kai wani hari a ranar litinin din da ta gabata da misalign karfe 8 na dare a garin Dumbin Rauga dake kan titin Kaduna zuwa Zaria, inda suka yi awon gaba da fiye da mutane 30.
Har zuwa yanzu rundunar ‘yan sanda ta jihar Kaduna ba ta ce komai kan lamarin ba.













































