Gwamnonin arewa maso gabas sun bukaci gwamnatin tarayya ta samar musu da wutar lantarki

northeast governor
northeast governor

Gwamnonin arewa wamnonin arewa maso gabashin Nigeria sun bukaci gwamnatin tarayya ta mayar da hankali wajen samar da wutar lantarki a yankin dake fama da matsalolin tsaro domin bunkasar tattalin arzikin arewa.

Bayanin hakan na kunshe ne cikin sanarwar bayan taro da aka fitar, bayan kammala taron kungiyar na karshen shekara.

Sanarwar wadda shugaban kungiyar ta gwamnonin arewa masu gasar kuma gwamnan Jihar Borno Babagana Zulum ya sanyawa hannu tace, babbar matsalar da yankin ke fama da ita shine rashin wutar lantarki, wanda hakan ke kawo koma baya ga bunkasar tattalin arziki tare da assasa rashin aikin yi sakamakon durkushewar kamfanoni.

Gwamnonin sun koka kan rashin kammala aikin wuta na Dadin Kowa da Kashimbila, inda suka bayyana a matsayin babban dalilin da ya jefa yankin cikin halin koma baya na tattalin arziki.

A bangaren, tsaro gwamnonin sun yabawa gwamnatin tarayya kan kokarin da take yi wajen ganin yankin na arewa masu gabas ya zauna lafiya, inda suka bukaci a samar da tsari na musamman ga tubabbun ‘yan tada kayar baya domin ganin basu kara komawa harkar ta’addanci ba.

Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da gwamnan jihar Borno Babagana Zulum, da gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni sai Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe da yayin da gwamnonin Bauchi da Adamawa da Taraba suka samu wakilcin mataimakan su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here