Gwamnatin jihar Kano ta hana amfani da jiragen ruwa na masu zaman kansu wajen jigilar fasinjoji a kogin Bagwai-Badau da ke karamar hukumar Bagwai ta jihar.
Idan na a mance ba a ranar Talata Solacebase ta ruwaito cewa wani jirgin ruwa dauke da fasinjoji kusan 50 ya kife da rayukan fasinjoji kusan 29, a kauyen Badau da ke karamar hukumar.
Ko a shekarar 2008 mutane 24 ne suka mutu a wani hatsarin jirgin ruwa a kauyen Badau a yayin daurin aure.
A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Malam Muhammad Garba ya fitar, ya ce a halin yanzu dai gwamnati ta samar da motocin bas guda biyu na jigilar fasinjoji tsakanin Badau da Bagwai, yayin da za a siyo sabbin jiragen ruwa guda uku domin tsallakar da mutane daga ruwa a yankin.
Sanarwar ta ce ana sa ran kaddamar da wasu matakan da suka dace idan kwamitin binciken da gwamnatin jihar ta kafa ya mika rahotonsa domin aiwatarwa.













































