Limamin kauyen Nghar da ke Karamar Hukumar Barkin Ladi a Jihar Plateau, Abubakar Abdullahi, wanda ya shahara yayin da ya tseratar da Kiristoci 262 a lokacin wani mummunan harin rikicin addini, ya rasu yana da shekaru 90.
Ɗansa, Saleh Abubakar, ya tabbatar da rasuwar limamin, inda ya bayyana cewa ya rasu a daren Alhamis a Asibitin Kwararru na Plateau da ke Jos bayan shafe kusan kwanaki goma yana jinya.
Rahotanni sun nuna cewa marigayin ya shafe lokaci yana fama da matsalar zuciya, lamarin da ya yi tasiri sosai ga lafiyarsa kafin rasuwarsa, inda ake duba lafiyarsa lokaci zuwa lokaci tun bayan gano cutar.
Marigayin ya bar ’ya’ya 19, ciki har da maza 12 da mata 7, wadanda ke ci gaba da tuna shi a matsayin uba mai tausayi da kishin bil’adama.
A watan Yuni na shekarar 2018, yayin da rikicin addini mai muni ya barke a kauyuka goma na Barkin Ladi, limamin ya boye Kiristoci 262 a masallaci da kuma gidansa har sai da tashin hankalin ya lafa, abin da ya ceci rayukansu daga kisan gilla.
Wannan aiki nasa ya jawo masa yabo a cikin gida da wajen Najeriya, inda aka karrama shi da lambar yabo ta ’yancin addini ta kasa da kasa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta bayar a shekarar 2019.
Rasuwar limamin ta bar gibi mai girma a zukatan al’umma daban-daban a Plateau da ma kasa baki daya, duba da rawar da ya taka wajen inganta zaman lafiya da hadin kai tsakanin mabiya addinai.













































