Kungiyar ma’aikatan lantarki a Najeriya (NUEE) ta sake barazanar kashe wutar kasar gaba daya idan gwamnati ta ki biyan bukatunta. Wannan ya biyo bayan karewar wa’adin makonni biyu da mambobin kungiyar suka baiwa gwamnati.
Sakataren Shirye-Shirye na yankin Arewa maso yamma, Dukat Ayuba, a hirar da yayi da manema labarai a Kaduna ranar Alhamis ya ce har yanzu suna tattaunawa amma zasu iya kashe wuta a koda yaushe.
Ayuba ya laburta cewa lamarin sayar da kamfanonin lantarkin duk damfara ne saboda shekaru 9 bayan haka babu sauyin da aka samu.
“Shi yasa muka ki yarda da sayar da kamfanonin raba lantarki, wadanda suka saya basu da karfi da ilimi. Mun baiwa gwamnati shawara amma ta ki.”
“Har yanzu da tsaffin injinan sama da shekaru 35, 40 zuwa 50 ake amfani. Abinda aka yi tsammani shine masu zuba jarin da suka saya zasu zuba sabbin kayan aiki amma babu abinda suka yi.”
Ya kara da cewa har yanzu megawatt 5000 na lantarki ake hakowa sama da shekaru 9, menene amfani sayar da kamfanin.
“Yanzu farashin lantarkin ya tashi. Hakan ya haifar da tsadar rayuwa ga miliyoyin yan Najeriya. Babu inda irin wannan abu zai faru illa Najeriya.” Inji shi.













































