Mataimakin shugaban ƙasa Shettima ya bar Abuja zuwa Guinea-Conakry

Shettima departs new 750x430

Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya bar Abuja domin wakiltar Shugaba Bola Tinubu a bikin rantsar da sabon shugaban ƙasar Guinea-Conakry, Mamadi Doumbouya, da za a gudanar a birnin Conakry.

Stanley Nkwocha, babban mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa a ofishin mataimakin shugaban ƙasa, ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar a Abuja.

Sanarwar ta bayyana cewa bikin rantsar da Mamadi Doumbouya, bayan nasararsa a zaɓe, zai gudana a ranar Asabar a filin wasa na GLC da ke Nongo a Conakry.

Halartar mataimakin shugaban ƙasa a bikin rantsarwar na da muhimmanci wajen ƙarfafa jagorancin yanki, bunƙasa haɗin gwiwar tattalin arziƙi, da haɓaka shigar ƙasashe cikin tattalin arziƙin duniya bisa tsarin sabunta manufa “Renewed Hope” na Shugaba Tinubu.

Ziyarar na kuma cikin rawar jagorancin Najeriya a ƙungiyar ECOWAS, musamman wajen tallafa wa Guinea-Conakry ta koma tsarin mulkin dimokiraɗiyya bayan shekaru huɗu na wa’adin sauyi, tare da ƙarfafa hulɗar kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu, inda fitar da kayayyakin Najeriya zuwa Guinea, musamman na masana’antu da noma, ya kai Dalar Amurka Miliyan 3.29.

Daga Guinea-Conakry, mataimakin shugaban ƙasa zai wuce Davos-Klosters a ƙasar Switzerland domin halartar taron shekara-shekara karo na 56 na kungiyar tattalin arzikin duniya na shekarar 2026, wanda zai gudana daga 19 zuwa 23 ga watan Janairu, inda zai tattauna da shugabannin duniya da masu zuba jari kan gyaran tattalin arziƙin Najeriya, damar zuba jari, da rawar Afirka a makomar duniya.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa taron World Economic Forum na 2026 mai taken “A Spirit of Dialogue” zai mayar da hankali kan tasirin sabbin fasahohi kamar basirar wucin-gadi ta AI, quantum computing, kimiyyar halittu ta zamani, da sabbin hanyoyin samar da makamashi, da kuma yadda za a yi amfani da su wajen samar da ci gaba mai ɗorewa da adalci.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here