Ma’aikatun tsaro da na harkokin cikin gida dole ne su yi aiki tare domin gyara giɓin tsaron Nijeriya – Musa

TAG07898 2048x1365 1 750x430

Ministan tsaro, Janar Christopher Musa, ya jaddada buƙatar ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ma’aikatar tsaro da ma’aikatar harkokin cikin gida, inda ya nuna cewa ƙalubalen tsaron cikin gida a Nijeriya ba za su samu mafita yadda ya kamata ba sai an yi aiki tare cikin cikakken haɗin kai da ɗaukar nauyi gaba ɗaya.

Musa ya gabatar da wannan matsaya ne yayin ziyarar girmamawa da ministan tsaro ya kai wa ministan harkokin cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, a Abuja, inda ɓangarorin biyu suka nuna aniyarsu ta ƙarfafa haɗin kai tsakanin ma’aikatunsu domin tinkarar barazanar tsaro da ke sauyawa a ƙasar.

Ministan tsaron ya bayyana ma’aikatun biyu a matsayin ginshiƙai biyu na tsaron ƙasa guda ɗaya, yana mai nuna cewa bambanci tsakanin tsaron cikin gida da na waje ya fara dusashewa sakamakon barazanar zamani kamar ta’addanci, tayar da ƙayar baya, fashi da makami da kuma laifukan ƙetare iyaka.

Ya kara cewa babu wata hukuma ko ma’aikata guda ɗaya da za ta iya magance irin waɗannan matsaloli ita kaɗai, tare da nuna muhimmancin tsarin tsaro na bai ɗaya wanda ya ta’allaka kan bayanan sirri, haɗin gwiwar gwamnati gaba ɗaya da kuma aiwatar da ayyuka cikin daidaito.

Ministan tsaron ya nuna buƙatar ƙarfafa haɗin gwiwa wajen bada bayanan sirri ta hanyar inganta tsarin haɗa bayanai tsakanin hukumar leƙen asirin tsaro da hukumomin karkashin ma’aikatar harkokin cikin gida, ciki har da hukumar shige da fice ta Nijeriya, hukumar tsaron fararen hula da kare kadarorin gwamnati da kuma hukumar gyaran hali.

Haka kuma, ya goyi bayan amfani da na’urorin fasaha masu tsaro domin musayar bayanai kai tsaye, gudanar da atisayen haɗin gwiwa akai-akai da kafa ƙa’idoji bayyanannu na ayyukan haɗin gwiwa domin rage cikas da inganta amfani da albarkatu.

Ya tabbatar da cewa ma’aikatar tsaro za ta ci gaba da tallafa wa hukumomin tsaron cikin gida ta fuskar gina ƙwarewa, horo na musamman kan yaƙi da ta’addanci, tattara bayanan sirri da martani ga rikice-rikice, tare da bayar da tallafin kayan aiki da na fasaha a duk inda buƙata ta taso.

Karanta: Zargin Almundahanar Naira Biliyan 1.35: Kotun koli ta umarci a ci gaba da shari’ar Sule Lamido da ’ya’yansa, ta juma tabbatar da hukuncin Aminu

A nasa ɓangaren, ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya nuna cewa raunin tsarin tsaron cikin gida kan ɗora nauyi mai yawa a kan sojoji, yana mai jaddada cewa ƙarfafa hukumomin tsaron cikin gida zai ba rundunar soji damar mai da hankali kan muhimmin aikin kare ƙasa.

Ya bayyana tsarin tsaron ƙasa a matsayin ginshiƙai uku da suka haɗa da bayanan sirri, tsaron cikin gida da tsaro na soja, inda ya nuna cewa rauni a ɓangare guda na iya girgiza tsarin gaba ɗaya.

Haka kuma, ya yi gargaɗi kan takaddama da ƙiyayya tsakanin hukumomin tsaro, yana mai jaddada cewa abin da ya fi damun ’yan Nijeriya shi ne tsaro da ingancin aiki, ba iyakokin ma’aikatu ba.

Ministan harkokin cikin gidan ya bayyana tsaron iyakoki a matsayin muhimmin fanni na haɗin gwiwa, musamman ta hannun hukumar shige da fice, yana mai nuna cewa babu ƙasar da za ta iya tabbatar da tsaron ’yan ƙasarta ba tare da kare iyakokinta ba.

Ya kuma fayyace rawar hukumar tsaron fararen hula da kare kadarorin gwamnati, yana mai jaddada cewa ba a kafa ta domin ta zama ’yan sanda na biyu ba, sai dai domin kare muhimman kadarorin ƙasa kamar makarantu, cibiyoyin mai da iskar gas, ma’adinai, hanyoyin sadarwa da wutar lantarki.

Ministocin biyu sun amince da muhimmancin haɗa bayanai a tsari guda, tare da nuna cewa rumbunan bayanai na ma’aikatar harkokin cikin gida ya kamata su zama muhimman ginshiƙai wajen tsara tsaro da yanke manyan shawarar tsaron ƙasa.

Sun kuma amince da kunna kwamitin fasaha na haɗin gwiwa tsakanin ma’aikatun domin rika taruwa akai-akai, tantance ci gaba, warware cikas da kuma ɗorewa da wannan haɗin gwiwa a matakan tsari da aiwatarwa.

Ministan tsaro da ministan harkokin cikin gida sun bayyana kwarin gwiwar cewa ci gaba da wannan haɗin gwiwa zai ƙarfafa tsaron ƙasa, ya ƙara amincewar jama’a da kuma samar da Nijeriya mafi aminci.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here