Mataimakin kwamishinan ƴan sanda ya mutu yayin taron gudanarwa – PPRO

POLICE OLOPA

Wani mataimakin kwamishinan ƴan sanda a jihar Ebonyi, ACP Ogbon-inu Popoola, ya rasu, yayin taron gudanarwa.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar SP Joshua Ukandu ya tabbatar da faruwar lamarin a garin Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi cikin wata sanarwa da ya fitar.

SP Joshua Ukandu, ya bayyana cewa marigayin ya rasu ne a ranar Laraba yayin da yake halartar taron gudanarwa na rundunar ƴan sanda ta jihar Ebonyi.

Rundunar ƴan sandan jihar Ebonyi ta bayyana alhini kan rasuwar marigayin, inda ta bayyana cewa ACP Ogbon-inu Popoola ya rasu a asibitin rundunar da ke hedkwatar ƴan sanda a Abakaliki.

Kafin rasuwarsa, shi ne mataimakin kwamishinan ƴan sanda mai kula da sashen tattara bayanan sirri na jihar.

Karanta: Bayelsa: PDP ta tabbatar da mutuwar mataimakin Gwamnan Jihar Lawrence Ewhrudjakpo

Rundunar ta bayyana cewa marigayin jami’i ne mai kwazo da sadaukarwa, wanda ya yi wa rundunar ƴan sanda aiki da cikakkiyar jajircewa da kwarewa a tsawon shekarun hidimarsa.

Wani babban jami’in ƴan sanda ya bayyana cewa marigayin ya fuskanci matsalar numfashi ba zato ba tsammani a yayin taron, lamarin da ya sa aka gaggauta kai shi asibitin rundunar a hedkwatar ƴan sanda ta Abakaliki, inda daga bisani ya rasu kamar yadda likita ya tabbatar.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa an ajiye gawar marigayin a dakin ajiyar gawawwaki na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Tarayya ta Alex Ekwueme da ke Abakaliki.

Rundunar ƴan sandan jihar Ebonyi ta miƙa ta’aziyya ga iyalansa bisa wannan babban rashi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here