Gwamnan jihar Filato Mutfwang ya koma APC

muftwang and apc

Jam’iyyar APC mai mulki ta sanar da sauya sheƙar gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Sauyin sheƙar ya ƙara girma ga jerin manyan ‘yan siyasa da suka bar babbar jam’iyyar adawa a ƙasar nan.

Shugaban APC na ƙasa, Nentawe Yelwata, wanda shi ma ɗan asalin jihar Plateau ne, ya bayyana hakan a taron majalisar koli na jam’iyyar karo na 14 da aka gudanar a Cibiyar Taro ta Fadar Gwamnati da ke Abuja.

Ya bayyana cewa sauya sheƙar gwamna Mutfwang na da matuƙar muhimmanci ga jam’iyyar.

Shugaban jam’iyyar ya ƙara da cewa bayan wannan sauyin sheƙa, yankin Arewa ta Tsakiya baki ɗaya yanzu yana ƙarƙashin shugabancin APC, lamarin da ya nuna ƙarfafa matsayar jam’iyyar a yankin.

An zaɓi gwamna Mutfwang ne a babban zaɓen shekarar 2023 a ƙarƙashin PDP, kuma ya zama ɗaya daga cikin fitattun shugabanni da suka fice daga jam’iyyar adawa zuwa APC a wannan lokaci.

A taron, shugaban APC ya ayyana ranar 30 ga watan Janairun 2026 a matsayin wa’adin ƙarshe da duk mambobin jam’iyyar za su kammala rijistar membobinsu.

Ya bayyana cewa tuni aka fara aiwatar da tsarin rijistar, kuma hakan zai ƙara gaskiya, ingancin bayanai da dimokuraɗiyyar cikin gida a jam’iyyar.

Ya kuma bayyana cewa an gudanar da horo a matakan jiha, shiyya-shiyya da ƙananan hukumomi a yawancin jihohi, tare da ƙarfafa duk masu ruwa da tsaki su tallafa wa yaɗa rijistar membobbin a faɗin ƙasa.

Ya buƙaci tsofaffi da sababbin mambobi su yi amfani da damar domin rijistar kansu da magoya bayansu, domin shiryawa manyan tarukan jam’iyyar da ke tafe.

Taron ya samu halartar Shugaban ƙasa Bola Tinubu, Mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shettima, shugabannin majalisar dokoki ta ƙasa, da tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Yemi Osinbajo, tare da gwamnonin APC, tsofaffin gwamnonin jihohi, shugabannin jam’iyyar na ƙasa da sauran manyan masu ruwa da tsaki a jam’iyyar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here