Gwamnan Kano ya jaddada kudurin gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar duk da dakatarwar kotu

Abba Kabir Yusuf 595x430

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da tutocin jam’iyyar NNPP ga ’yan takarar shugabancin kananan hukumomi 44 na jam’iyyar domin zaben kananan hukumomin da za a gudanar nan ba da jimawa ba.

Duk da hukuncin kotu da ya dakatar da zaben, gwamnan ya tabbatar wa mambobin jam’iyyar cewa za a ci gaba da zaben kamar yadda aka tsara, tare da jaddada cewa “ba za a ja da baya ba.”

Wannan matakin ya biyo bayan hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Kano a ranar Talata, wadda ta cire Farfesa Sani Malunfashi da wasu mutum biyar daga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kano (KANSIEC) tare da dakatar da zaben ranar 26 ga Oktoba.

Da yake jawabi a taron da aka yi a Filin Wasan Cikin Gida na Sani Abacha, Gwamna Yusuf ya jaddada kudurin jihar na ci gaba da kwanciyar hankali, yana mai cewa KANSIEC na da cikakken ikon gudanar da zaben bisa kundin tsarin mulki.

Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin, ya nakalto Yusuf yana cewa babu wanda zai hana KANSIEC gudanar da aikin da aka dora mata.

Yusuf ya bukaci mambobin NNPP su kara kaimi wajen samun goyon bayan jama’a a mazabunsu, yana mai fatan jam’iyyar za ta lashe kujeru 44 na shugabancin kananan hukumomi da kujeru 484 na kansiloli.

A taron, Shugaban riko na kasa na NNPP, Dokta Audu Ajuji, Shugaban NNPP na jihar Alhaji Hashim Sulaiman Dungurawa, tare da ‘yan majalisar jiha da ta tarayya, kwamishinoni, mashawarta na musamman da sauran manyan ‘yan jam’iyya sun halarta.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here