Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ya bayyana dalilin tsayar da Mustapha Gubio a matsayin wanda yake so ya gaje shi gabanin zaben gwamna na shekarar 2027.
Zulum ya yi wannan bayanin ne a Abuja yayin da yake mika wa Gubio fom din nuna sha’awa da tsayawa takara na jam’iyyar APC.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Dauda Iliya, ya fitar a ranar Laraba, gwamnan ya ce matakin na da nufin ci gaba kan irin ci gaban da aka samu a karkashin gwamnatinsa.
“Na san yadda na shigo a matsayin kwamishinan sake ginawa da gyara matsugunni (Reconstruction, Rehabilitation and Resettlement) da ake yi wa lakabi da RRR. Da yadda ofishin ya sauya tsarin shugabanci wanda ya sauya rayuwar al’ummarmu. Saboda irin yadda Injiniya Gubio ya nuna irin kwarewa da sadaukarwa ta musamman ga aikin gwamnati,” in ji Zulum.
Zulum ya kara da cewa Gubio ya nuna kwarewa ta musamman wajen sanya ido kan muhimman ayyukan gine-gine, musamman gina gidaje a fadin birane da na karkara, wanda ya inganta yanayin rayuwa a jihar.
A cewar sanarwar, Gubio ya jagoranci sake gina yankunan da rikici ya shafa kamar kananan hukumomin Bama, Konduga, Damasak da Mafa, inda ya tabbatar da maido da makarantu, cibiyoyin kiwon lafiya da sauran muhimman ayyuka.
Zulum ya ce nasarorin sun yi daidai da hangen nesan gwamnatinsa na farfadowa da zaman lafiya da ci gaba mai dorewa, inda bayyana Gubio a matsayin zabin da ya dace don ƙarfafa ci gaban da ake samu.
Gwamnan ya jaddada cewa amincewar wani mataki ne na dabara wanda ya dogara da ci gaba, gogewa da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya, juriya da shugabanci mai sauyi a Borno. (NAN)











































