Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya amince da kwamitin da aka kafa domin gudanarda wani bincike a jami’ar kimiyya da fasaha dake Wudil.
Sanarwar da Kwamishinan Yada Labarai, Malam Muhammad Garba ya sanyawa hannu, ta ce matakin ya biyo bayan shawararwi kan rahoton kwamitin ziyarar jami’ar da majalisar zartarwa ta jihar ta amince da gudanarwa a yi.
Sanarwar ta ce kwamitin zai binciki dukkanin bashin da ake bin su, da asusun da aka tantance tare da kwato kudaden da aka batar a jami’ar.
Ya bayyana cewa kwamitin zai kasance karkashin jagorancin Babban Sakatare na ofishin shugaban ma’aikata.
Sanarwar ta ce sauran mambobin kwamitin sun hada da babban sakatare na ofishin sakataren gwamnatin jihar; Sakatare na dindindin, Asusun Amintattun Yan Fansho; Babban Sakatare da Ma’aikatar Kudi; Babban mai binciken kudi na jiha.
‘’Sauran su ne mai binciken kananan hukumomi, shugaban hukumar korafe-korafen jama’a da kuma yaki da cin hanci da rashawa; Babban Sakatare a Ma’aikatar Ilimi; yayin da Babban Sakatare, Ma’aikatar Shari’a, zasu zamo memba kuma sakataren kwamitin, ” in ji sanarwar.
‘’ Ana sa ran Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne zai kaddamar da kwamitin nan gaba kadan da za sanar”.













































