Sanatoci uku na jam’iyyar APC sun yi fice daga jam’iyyar mai mulki.
Sanatocin da suka fita sun haɗa da: Ahmad Babba Kaita (Katsina ta Arewa), Lawal Gumau (Bauchi ta Kudu) da Francis Alimikhena (Edo ta Arewa).
Sanarwar ficewar da sukayi na ƙunshe ne a cikin wasiku da ko wannen ya aike wa shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan ya kuma karanta yayin zaman majalisar a yau Talata.
Yayin da Kaita da Alimikhena suka sauya sheka zuwa babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Gumau, ya koma jam’iyyar NNPP.













































