Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta sanar da sakin tsohon sakataren kwallon kafa ta najeriya NFF, Alhaji Sani Toro, tare da mataimakin mai horas da ‘yan wasan Super Eagles Alhaji Isa Jah, daga hannun masu garkuwa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, SP Ahmed Wakil ne ya tabbatar da sakin nasu, ya ce har yanzu ba cikakken bayani akan yace aka sake su.
Kamfanin dillancin labarai NAN, ya rawaitu cewa an yi garkuwa dasu ne ranar Asabar, yayin da suke kan hanyar su ta dawo wa daga Abuja.












































