Majalisar dattijai ta nada sabon shugaban marasa rinjaye, tare da mai tsawatar wa bangaren marasa rinjaye

Senate
Senate

Majalisar dattije ta sanar da nada sanata Philip Aduda, a matsayin shugaban marasa rinjaye na majalisar.

Ta kuma sanar da sanata Chukwuka Utazi, a matsayin mai tsawatarwa bangaran marasa rinjaye.

Sanawar na dauke cikin wasikar da sakataran jam’iyyar PDP, sanata Samuel Anyanwu ya aikewa shugaban majalisar.

Kamfanin dillancin labarai NAN ya ruwaitu cewa an nada Aduda dan ne, biyu bayan fitar tsohon shugaban marasa rinjaye sanata Eyinnaya Abaribe daga APGA zuwa PDP

Shugaban majalisar ya taya su murna bisa nadin da akayi musu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here