Shugaban kasa Buhari zai tafi kasar Rwanda

Buhari departs
Buhari departs

Shugaban kasa Muhammadu Buhari   zai tafi birnin Kigali da ke kasar Rwanda a yau Laraba, domin halartar taron CHOGM 2022.

Hakan na  dauke cikin wata sanar wa da mai bawa shugaban kasa shawara akan harkar yada labarai, Femi Adesina ya fitaar.

Taron mai laƙabin CHOGM 2022, zai tattauna kan halin rayuwa da kuma ci gaban al’ummar ƙungiyar fiye da biliyan biyu da ke zaune a ƙasa 54 na nahiyoyin Afirka da Asiya da Amurka da Turai da kuma yankin Pacific.

Sanarwar taci ana sa rai shugaban kasar zai yi jawabi a gurin taron, sannan kuma zai gana da shugabanin da suka halar ci taro

taron dai an fara gudanar dashi tun daga 20 zuwa 26 ga watan June na shekarar 2022.

Shugaban kasar zai sami rakiyar ministan harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama, ministan lafiya, Osagie Ehanire, Mohammed Abdullahi, ministan kudi, Zainab Ahmed da kuma ministan sadarwa, Isa Ali Pantami.

Sauran ‘yan tawagar sun hada da Ahmed Rufa’i Abubakar, Abike Dabiri-Erewa da  kuma mai bawa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro Maj-Gen Babagana.

Sanarwar ta kara da cewa shugaban kasar zai dawo Abuja ranar Lahadi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here