Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa sun yi ba dadi da Asiwaju Bola Tinubu a shekarar 2007, bisa yunkurin da ya yi na neman tikitin takarar Musulmi da Musulmi gabanin zaben shugaban kasa da aka yi a watan Afrilun shekarar 2007.
Atiku ya bayyana hakan ne ranar Juma’a, a wata hira da gidan talabijin na Arise wadda Jaridar Solacebase ta bibiya.
Ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya dade yana makance da yawaitar addinai a Kasar nan kuma yana goyon bayan tsayar da ‘yan takarar shugaban kasa mabiya addini daya.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana rashin jin dadinsa game da yadda wasu fusatattun mutane suka nuna bacin ransu bayan matakin da Tinubu ya dauka na zabar dan uwansa musulmi, Sanata Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa a zaben shugaban kasa na 2023.
A cewarsa, “Babban sabani na da Asiwaju (Bola Tinubu) tun a shekarar 2007 shi ne batun tikitin tikitin Musulmi da Musulmi.
Wannan shi ne babban rashin jituwa ta da Asiwaju a siyasance,” in ji Atiku, yayin da ya zargi gwamnatin APC karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari da bada gudunmawa wajen tabarbarewar hadin kai da zumunci a tsakanin ‘yan kasa.
“Ku tuna cewa na fito daga PDP (na sauya sheka) kan batun shiyya-shiyya kuma tare da Asiwaju muka kafa jam’iyyar ACN, aka bani tikintin takara a Legas, shi kuma (Tinubu) ya dage cewa zai zama abokin takarata. Na ce a’a! Ba zan samu yi tikitin musulmi da musulmi ba, saboda haka ya sauya sheka zuwa ga marigayi Umaru Yar’adua. Wannan shi ne dalilin rabuwar mu.

Atiku ya ci gaba da cewa, kin amincewar da ya yi na tikitin takarar Musulmi da Musulmi bayan jam’iyyun ACN da CPC da suka hade suka kafa APC ya hana Buhari zabar Tinubu, Musulmi a matsayin abokin takararsa.
Turakin Adamawa ya kuma amsa tambayar da aka yi masa akan ko matakin da Tinubu ya dauka na zabar wanda zai tsaya takara daga yankin Arewa maso Gabas ba zai yi tasiri a zaben sa ba tunda shi (Atiku) ya fito daga Arewa maso Gabas.
Idan dai za a iya tunawa dai Tinubu ya ce bai dauki matakin da ya dauka na zaben dan uwa musulmi a matsayin abokin takararsa ba “a kan addini ko don faranta wa wata al’umma ko wata kabila rai ba”. “Na yi wannan zabin ne saboda na yi imani wannan shi ne mutumin da zai iya taimaka min wajen kawo kyakkyawan shugabanci ga daukacin ‘yan Najeriya, ba tare da la’akari da addini ko kabilanci ko yanki ba, Tinubu ya bayyana haka ne a wajen kaddamar da Shettima a matsayin Dan takarar mataimakin shugaban kasa.













































