Shugaba Bola Tinubu ya nada Misis Bianca Odumegwu-Ojukwu a matsayin ministar harkokin waje, bayan murabus din Amb. Yusuf Tuggar.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Mista Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Laraba a Abuja.
Tuggar ya yi murabus ne domin shiga zaben shekarar 2027 mai zuwa.
Odumegwu-Ojukwu ta taba zama karamar ministar harkokin waje a baya.
Haka kuma, shugaban ya zabi Amb. Sola Enikanolaiye a matsayin karamin ministan harkokin waje, wanda shima yake jiran tabbatarwa daga majalisar dattawa.
Kafin nadin nasa, Enikanolaiye, ya rike mukamin babban mataimaki na musamman ga shugaban Ƙasa kan harkokin waje da dangantakar kasa da kasa.
Fadar shugaban kasa ta bayyana Enikanolaiye a matsayin fitaccen jami’in diflomasiyya kuma kwararren ma’aikacin gwamnati da ke da gogewar sama da shekaru talatin a harkar diflomasiyyar Najeriya.
Ya taba rike mukamin babban sakatare a ma’aikatar harkokin waje.
Ya kuma rike mukaman diflomasiyya a Addis Ababa, Belgrade, Ottawa, London da New Delhi.
Tinubu ya ce nade-naden na daga cikin kokarin da ake ci gaba da yi na sake fasalin tsarin manufofin harkokin wajen Najeriya.
Ya ce matakin zai habaka inganta dabaru da karfafa hadin gwiwar duniya.
Shugaban ya taya wadanda aka nada murna kuma ya bukace su da su yi aiki tukuru wajen bunkasa muradun Najeriya.
Ya kuma umurce su da su ciyar da diflomasiyyar tattalin arziki gaba, da samar da zaman lafiya a yankin da tabbatar kare jin dadin ‘yan Najeriya a gida da kasashen waje. (NAN)











































