Mista Eseme Eyiboh, mashawarcin shugaban majalisar dattawa na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, ya karyata rahotannin da ke cewa an samar da ofishi ga uwargidan shugaban majalisar dattawa, Misis Unoma Akpabio, a majalisar dattawan kasar.
Eyiboh, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin a Abuja, ya ce labarin ya nuna cewa da gaske an yi shi ne domin yin batanci da kuma tozarta shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio.