Hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci ta Kano ta kwato sama da Naira Miliyan 40, ta miƙa su ga mamallakansu

WhatsApp Image 2025 12 18 at 20.13.18 750x430

Hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci ta jihar Kano ta kwato sama da Naira Miliyan 40 daga rikice-rikicen kasuwanci da mu’amaloli daban-daban, sannan ta miƙa ceki ga waɗanda kuɗaɗen suka shafa.

Matakin ya zo ne domin nuna nasarorin da hukumar ke samu tare da ƙarfafa jama’a su nemi hakkinsu ta hanyoyin doka.

Shugaban hukumar, Malam Sa’idu Yahaya, ya jagoranci miƙa ceki ɗin a hedkwatar hukumar da ke Kano ranar Alhamis.

Ya bayyana cewa kwato kuɗaɗen wani ɓangare ne na ayyukan yau da kullum na sasanta rikice-rikice tsakanin daidaikun mutane da ƙungiyoyi, bisa ikon da dokar hukumar ta shekarar 2008, da aka yi mata gyara, ta tanada.

Ya jaddada cewa hukumar na sasanta rikice-rikicen farar hula ne kawai, musamman waɗanda suka shafi mu’amalar kasuwanci, ba tare da shari’o’in laifi ba.

A cewarsa, kasancewar Kano cibiyar kasuwanci ce, rikice-rikice kan taso a harkokin kasuwanci, kuma rawar hukumar ita ce taimaka wa ɓangarori su cimma matsaya ta doka.

Daga cikin kuɗaɗen da aka miƙa akwai Naira Miliyan 2 ga Kamfanin Karry Consult da Kamfanin Fam Nigeria Limited, Naira Miliyan 1 ga Nuradeen Usman Usman, da kuma Naira Miliyan 17 ga Kamfanin AbdulHakim da Brothers Enterprise, tare da wasu makamantansu.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa shugaban hukumar ya bayyana cewa adadin kuɗaɗen da aka kwato a wannan rana kaɗai ya kai kusan Naira Miliyan 40, wanda na faruwa kusan kullum, sai dai ba a cika bayyana su a bainar jama’a ba.

Ya kuma bayyana cewa wannan ne karo na farko da ake miƙa ceki tun bayan da ya karɓi muƙami a watan Agusta, inda ya nuna cewa a baya ana mayar da kuɗaɗen ta hanyar canja wurin kuɗi kai tsaye ta banki domin rage hulɗar kai tsaye.

A cewar sa, miƙa cekin a fili an yi shi ne domin nuna buɗaɗɗiyar hanya da shirye-shiryen hukumar wajen karɓar ƙorafe-ƙorafe cikin gaskiya da bin doka.

Shugaban hukumar ya tabbatar wa jama’a cewa hukumar za ta ci gaba da aiki bisa gaskiya, ƙwazo da adalci wajen sauraron ƙorafe-ƙorafe, tare da kiran mutane da ƙungiyoyi masu irin waɗannan rikice-rikice su tunkari hukumar domin a warware su ta doka.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here