Majalisar dokokin jihar Kwara ta dakatar da Hon. Yisa Gideon na APC mai wakiltar Edu na tsawon watanni uku bisa wani zargin aikata abin da ake kallo a matsayin raina majalisar, duk da cewa ba a fayyace irin laifin ba.
An ɗauki matakin ne a zaman majalisar da aka gudanar a birnin Ilorin.
Kakakin majalisar, Yakubu Danladi-Salihu, ya bayyana cewa dakatarwar ta fara aiki nan take.
Ya ce an yanke hukuncin ne bisa tanadin sashe na 14 ƙaramin sashe na biyu na dokar ikon da martabar majalisun dokoki ta shekarar 2017.
Ya kuma umarci Hon. Yisa Gideon da ya rubuta wasiƙar neman afuwa ga majalisar yayin da yake cikin dakatarwar.
Wannan umarni ya zo ne a matsayin wani ɓangare na matakan da majalisar ta ɗauka domin kare mutunci da martabarta.
Yayin gabatar da kudirin ba tare da sanarwa ba, jagoran majalisar, Abdukadir Mogaji, ya bayyana cewa an bai wa ɗan majalisar damar kare kansa yadda ya kamata, ai dai bai bayyana takamaiman abin da ya haifar da zargin raina majalisar ba.
Mogaji ya ƙara da cewa an ba Gideon damar bayyana gaban wani kwamitin wucin gadi da majalisar ta kafa domin amsa tuhumar da ake yi masa.
A cewarsa, ɗan majalisar ya amince da aikata laifin da aka danganta masa.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa majalisar ta dauki matakin ne bayan kammala dukkan hanyoyin doka da tanadi, domin tabbatar da bin ka’ida da kare tsarin aiki na majalisar dokokin jihar Kwara.













































