An kashe mutane 2 da kone gidaje a rikicin kabilanci a jihar Benue

rikin kabilanci, kashe, mutane, kona, gidaje, jihar, Benue
Rahotanni sun ce an kashe mutane biyu tare da harbe wasu biyu da kona gidaje a wani rikicin kabilanci da ya rutsa da al’ummar Ajetachi a yankin Bankin Arewa...

Rahotanni sun ce an kashe mutane biyu tare da harbe wasu biyu da kona gidaje a wani rikicin kabilanci da ya rutsa da al’ummar Ajetachi a yankin Bankin Arewa da ke wajen Makurdi, babban birnin jihar Benue.

A cewar shaidun gani da ido, rikicin ya faru ne da yammacin ranar Lahadi har zuwa ranar Ista ta Litinin inda aka kona gidaje da dama yayin da lamarin ya faru.

Wani ganau, Nura Umah, ya shaidawa manema labarai cewa rikicin ya kasance tsakanin matasan Jukun da Tibi.

Karin labari: Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da fashewar wani abu a karamar hukumar Ikeja

“Rikicin ya faro ne da yammacin ranar Lahadi tsakanin matasan Jukun da Tibi, an kona gidaje da dama a Ajetachi, kusa da tsohuwar gada a bankin Arewa.

“Mutane biyu ne suka mutu a rikicin, daya daga cikinsu (wanda ya rasu) direban okada ne, da kuma wani mutum da ya rika safarar fata.

Karin labari: Majalisar wakilan Najeriya na shirin kwato jirage 2 na NCAT Zariya da aka sayar

“Sun yi jana’izar mutanen biyu a yau (Litinin), jiya a lokacin da Jukuns suke cikin cocin, ‘yan kabilar Tibi suka far musu a cocin, suka harbe mutane biyu da ke karbar magani a asibiti a halin yanzu.” Inji Umar.

An yi kokarin samun jin ta bakin kwamishinan ‘yan sandan, Emmanuel Adesina, amma hakan ba ta samu ba, sai dai yayin kiran wayar ta yi ringi amma babu masa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here