Wanda ya zana tutar Najeriya, Akinkunmi, ya rasu yana da shekaru 87

0
Taiwo Akinkunmi

Wanda ya zana tutar Najeriya mai suna “Green-White-Green” mai alamar zaman lafiya da noma, Pa. Taiwo Akinkunmi ya rasu.

Rahotanni sun bayyana cewa Pa. Akinkunmi ya rasu ne a safiyar ranar Talata bayan gajeriyar rashin lafiya, yana da shekaru 87 a duniya.

Daya daga cikin ‘ya’yansa ya tabbatar da rasuwarsa a wani sakon da ya wallafa a Facebook.Ya rubuta: “Hakika rayuwa mai wucewa ce; Zan iya faɗi da ƙarfin hali cewa kuna rayuwa tare da alamar ƙasa.

Murgayin Ya halarci makarantar Baptist Day da ke Ibadan inda ya yi karatun firamare da kuma makarantar Grammar ta Ibadan da ke Ibadan domin yin karatunsa na sakandare.

Pa Akinkunmi ya fara aikinsa ne a matsayin ma’aikacin gwamnati a sakatariyar birnin Ibadan, daga nan kuma ya tafi kasar waje inda ya karanci Injiniyan Aikin Noma a Kwalejin Fasaha ta Norway.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here