Hukumar da ke kula da gidajen ajiya da gyaran hgyaran hali ta kasa NCoS ta bayyana cewa adadin fursunonin da aka yanke musu hukuncin kisa ya karu daga 3,590 a watan Satumban 2024 zuwa 3,688 a watan Maris na 2025, wanda ya nuna karuwar kashi 2.73 cikin 100 ko kuma fursunoni 98 cikin watanni shida.
Hukumar ta NCoS ta kuma nemi hadin gwiwa tare da rundunar ‘yan sandan da DSS da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC) da hukumar yaki da cin janci da rashawa (ICPC) don hanzarta tafiyar da harkokin shari’a a kasar nan.
Mukaddashin Konturola-Janar na NCoS Sylvester Nwakuche ne ya bayyana hakan a jiya yayin da kwamitin majalisar dattijai mai kula da harkokin cikin gida, karkashin jagorancin Sanata Adams Oshiomhole, ke tantance shi a kan mukamin babban konturola.
Nwakuche ya samu rakiyar babban hadimin sa Godwin Okosun da mataimakin Konturola na hukumar NCoS da Babatunde Ogundare; mukaddashin Konturola-Janar na NCoS Sylvester Nwakuche da mataimakin Konturola janar na NCoS Ahmed Adagiri, da dai sauransu, wajen aikin tantancewar
Karin karatu: Ambaliyar ruwa: Fursunoni sama da 200 sun tsere daga gidan gyaran hali a Maiduguri
Da yake amsa tambayoyi a wurin tantancewar tare da hujjoji da ƙididdiga a jiya, Nwakuche ya bayyana cewa aƙalla fursunoni 3688 ne ke fuskantar hukuncin kisa a ƙasar nan idan aka kwatanta da 3,590 da ake da rahoton su a watan Satumban 2024.
Ya bayyana manyan kalubalen da hukumar gyaran ke fuskanta a kasar nan, inda ya bayyana cewa yawancin fursunonin “a halin yanzu suna jiran hukunci. Wannan shine babban kalubalen da muke ƙoƙarin magancewa a kullum.
Mukaddashin babban kwanturolan ya ce, Fursunonin da ake yanke wa hukuncin kisa yanzu sun kai 3688 daga 3,590 a watan Satumban 2024. Gwamnonin jihohi na daga cikin kalubalen da muke fuskanta. Sun ki zartar da hukuncin kisa ga fursunoni; haka kuma ba su mayar da hukuncin kisa zuwa daurin rai da rai ba.
Sai dai ya yi alkawarin hada kai da sauran hukumomin tsaro cikin dabara don ganin an warware matsalolin da ake jira na shari’a ta yadda za a iya rage cunkoso a gidan yarin.