Jami’an tsaro sun hana Fubara shiga majalisar dokokin jihar Rivers

Siminalaye Fubara 750x430

Jami’an tsaron da ke gadin harabar majalisar dokokin jihar Rivers sun ƙulle ƙofar majalisar tare da hana gwamnan jihar Siminalayi Fubara shiga zauren majalisar.

Cikin wani bidiyo da sakataren yaɗa labaran gwamnan ya wallafa shafinsa na Facebook ya ce Fubara ya je majalisar ne domin gabatar da kasafin kuɗin jihar na 2025.

Rahotonni daga birnin Fatakwal sun ce tarin jami’an tsaron da aka jibge a harabar sun rufe ƙofar shiga majalisar a lokacin da gwamnan ya hallara tare da tawagarsa domin gabatar da kasafin.

Bayanai sun ambato jami’an tsaron na cewa sun yi hakan ne saboda ba a sanar da su labarin zuwan gwamnan a hukumance ba.

Karin karatu: Rivers: APC ta buƙaci Fubara ya yi murabus ko a tsige shi

To sai dai Gwamna Fubara ya ce tuni ya aike wa kakakin majalisar, Martins Amaewhule wasikar sanar da shi zuwansa, kuma ya yi ƙoƙarin kiransa a waya tun ranar Talata.

A makonnin da suka gabata ne dai Kotun Ƙolin ƙasar ta yanke hukunci hana CBN bai wa jihar kason kuɗaɗenta daga tarayya saboda rashin gabatar da kasafin kuɗi a gaban halastacciyar majalisar dokokin jihar.

Haka kuma kotun ta yanke hukuncin maido da ƴanmajalisar jihar 27 da suka sauya sheƙa zuwa APC, tare da soke zaɓen ƙananan hukumomin jihar.

To sai dai a ranar 28 ga watan Fabrairu, Fubara ya sanar da yin aiki da hukuncin kotun tare da umartar hukumar zaɓen jihar ta shirya sabon zaɓen ƙananan hukumomin.

Tuni dai hukumar ta saka ranar 9 ga watan Agustan 2025 domin gudanar da sabon zaɓe.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here