Auren Zaurawa: Gwamnatin Kano Ta Kashe Naira Miliyan 800 Wajan Siyan Kayan Daki da sauran Kayayyaki Na  Ma’aurata 1,800

Mass Wedding 750x430
Mass Wedding 750x430

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta sayo kayan daki da sauran kayan daurin auren ma’aurata 1,800 a karkashin shirinta na daurin Zaurawa.

Babban kwamandan hukumar Sheikh Aminu Daurawa ya bayyana haka a lokacin da ya duba wasu kayayyakin da aka siyo domin rabawa amaren da za a daura auren su a ranar Laraba a Kano.

Ya ce gwamnati ta ware sama da Naira miliyan 800 don siyan kayan sawa, kayan abinci, kayan daki, da sauran kayayyakin bukatu na bikin aure.

“Kowace Amarya za ta samu katifa, matashin kai, da kuma Naira 20,000 domin fara sana’a.

“Wasu masu hannu da shuni sun yi alkawarin bayar da gudummawar kason su don ganin an samu nasarar daurin auren.”

“Ma’aurata 1,800 za su amfana da wannan karimcin, wanda zai taimaka matuka wajen dakile munanan dabi’u da fatara a tsakanin al’umma.” inji shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here