Gwamnatin kano ta bayyana damuwar ta kan rashin malamai a makarantu 400 da suke Kano ta Arewa

Abba Kabir Yusuf
Abba Kabir Yusuf

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana damuwarta kan yadda aka gano cewa sama da makarantu 400 ne ke da malami daya kacal a kowace makaranta a Kano ta Arewa.

SOLACEBASE ta ruwaito Kwamishinan Ilimi na jihar Alhaji Umar Haruna Doguwa ya koka da hakan a wani taro da ma’aikatan hukumomi biyar da ke karkashin ma’aikatar sa da aka gudanar a Rumfa Collage, Kano, ranar Talata.

Doguwa ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf yana da cikakkiyar masaniya game da durkushewar fannin ilimi gaba daya wanda hakan na da alaka da rashin nuna damuwa da jajircewa daga gwamnatin da ta gabata ta yi.

Ya bayyana cewa daga binciken da aka gudanar ya zuwa yanzu, akwai sama da dalibai miliyan hudu a fadin jihar da ke zaune a kasa yayin da wasu makarantun ke da malami daya kacal, lamarin da ya bayyana a matsayin abin tausayi.

A cewar Kwamishinan, jihar na daukar kwararan matakai domin kawo dukkan sauye-sauyen da za a iya samu a fannin ilimin firamare da sakandare na jihar.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here