A safiyar Larabar nan ne hafsoshin sojojin kasar Gabon karkashin kwamitin mika mulki da maido da hukumomi suka bayyana a gidan talabijin na kasar dalilin da ya sa suka karbar mulki daga hannun shugaba Ali Bongo a kasar.
Sojojin sun bayyana munanan rikice-rikice na hukumomi, tabarbarewar siyasa, tattalin arziki da zamantakewa a matsayin abubuwan da suka haifar da juyin mulkin da suka kira.
“A yau, kasar nan na cikin mawuyacin hali na rikice-rikice na hukumomi, siyasa, tattalin arziki da zamantakewa.
“Don haka an tilasta mana mu yarda cewa shirya babban zaɓen ranar 26 ga watan Agusta, 2023, bai cika sharuddan gudanar da zaɓe na gaskiya, sahihanci da haɗa kai da jama’ar Gabon ke fata ba.













































