A yau Laraba ne majalisar dokokin jihar Zamfara ta tsige mataimakin gwamnan jihar Mahdi Aliyu Gusau.
A zaman da aka yi a ranar Laraba, 21 daga cikin 21 ‘yan majalisa ne suka kada kuri’ar amincewa da kudirin.
Solacebase ta ruwaito cewa kwamitin binciken tsige mataimakin gwamnan mutum bakwai, ya mika rahotonsa a ranar Litinin ga kakakin majalisar.
Muna tafe da cikakkun bayani nan gaba.













































