Zamfara: Gwamna Matawalle ya mika sunan sabon mataimakinsa ga majalisar dokokin jihar

Senator Muhammad Hassan Nasiha
Senator Muhammad Hassan Nasiha

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya aikewa majalisar dokokin jihar sunan Sanata Muhammad Hassan Nasiha a matsayin mataimakin gwamnan jihar.

A zama na biyu da majalisar ta yi a yau, kakakin majalisar, Nasiru Mua’zu, ya karanta wasikar da gwamna Bello Matawalle ya aiko wadda ta bayyana tsayar da Sanata Muhammad a matsayin mataimakin gwamnan jihar Zamfara.

Solacebase ta ruwaito cewa Wannan na zuwa ne sa’o’i bayan majalisar ta tsige Mahdi Gusau a ranar Laraba.

Sanata Hassan shine dan majalisar wakilai mai  wakiltar mazabar Zamfara ta tsakiya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here