Majalisar Wakilan Najeriya ta bada umarnin gudanar da bincike kan musababin wahalar da alhazan Najeriya suka sha a Saudiyya ya yin Hajjin bana.
Hakan ya biyo bayan wani kudiri da wani dan majalisar, Ahmed Idris ya kai gaban zauren majalisar a ranar Alhamis.
Idon zaku iya tunawa a baya, wanda ya jagoranci tawagar likitocin Najeriya, Dakta Usman Galadima ya ce alhazan Najeriya bakwai ne suka mutu a filin Arfa.
Inda yace alhazan sun fito ne daga jihohin Plateau; Kaduna; Osun; Borno; Yobe; Abuja; Benue; da kuma Lagos.
A wani rahoton alhazan Najeriya da dama sunyi korafin ba’a basu wadatatcen masauki ba da kuma kin basu wadatatcen abincin da zai wada ce su ya yin zaman su a Mina.













































