Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta shiyyar Kano ta gurfanar da Sulaiman Inuwa Zakiru da Aliyu Ahmed a gaban wata babbar kotun jihar Kano karkashin mai shari’a Amina Adamu Aliyu bisa tuhume-tuhume biyu da suka hada da laifin hada baki da kuma karbar kudi ta hanyar karya.
SolaceBase ta ruwaito cewa wadanda ake zargin sun hada baki ne wajen yin kamanceceniya da Alhaji A.A. Rano, fitaccen dan kasuwar man fetur kuma mai kamfanin A.A.Rano Oil and Gas Limited inda suka damfari wadanda abin ya shafa zunzurutun kudi har Naira miliyan 12,000 (Naira miliyan goma sha biyu) domin biyan wani kason mai da aka ce A.A Rano Oil and Gas ya bayar.
Babban wanda ake zargin, Sulaiman Inuwa Zakiru, ya yi zargin cewa ya damfari mai kara da cewa A. A. Rano zai tuntube shi bayan ya kai wa dillalan man din ziyarar ban girma.
Daga nan sai wani da ke ikirarin cewa shi ne A. A Rano ya kira mai karar ya ba shi kayan man fetur a kan kudi Naira miliyan 12,000,000.
Bayan ya biya shi kudin a wasu asusu guda biyu na banki masu dauke da suna ‘A.A Yansamary General Enterprise da Zahda General Enterprise’ daga karshe mai shigar da karar ya gana da ainihin A. A Rano inda suka sanar da shi cinikin, amma dan kasuwar ya musanta cewa bai san maganar ba.
Wadanda ake tuhumar dai sun ki amsa laifin da ake tuhumarsu da shi lokacin da aka karanta musu.
Dangane da kokensu, lauyan masu shigar da kara, Zarami Mohammed, ya bukaci a sanya ranar shari’a sannan ya bukaci kotun da ta ci gaba da tsare wadanda ake kara a gidan gyaran hali har sai an fara shari’a.
Don haka, Mai shari’a Aliyu ya dage sauraron karar har zuwa ranar 22 ga watan Mayun 2025, domin a fara shari’ar tare da bayar da umarnin a tsare wadanda ake kara a gidan gyaran hali.













































