Kungiyar da ke sanya ido kan ayyukan majalisun dokoki da yaki da cin hanci da rashawa (CISLAC) ta rattaba hannu a kan wata takardar yarjejeniya da hukumar Korafe-korafen Jama’a da yaki da din hanci da rashawa ta Jihar Kano don tabbatar da bin diddigin kadarori da kwato su a jihar Kano.
Yarjejeniyar ta hada da hadin gwiwa don tabbatar da cewa an kare masu fallasa bayanai ta hanyar amfani da hanyoyin da ake da su da kuma tsare-tsare na shari’a a cikin rashin ingantaccen tsarin doka da kuma nuna gaskiya game da sanya jama’a a cikin harkokin mulki.
SolaceBase ta ruwaito cewa yarjejeniyar da aka sanya wa hannu a hedikwatar hukumar da ke Kano a ranar Alhamis ita ce don karfafa yaki da cin hanci da rashawa da kuma karfafa nasarorin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta samu kan gaskiya da kuma cimma muradun ci gaba mai dorewa.
Da yake jawabi a wajen taron, Babban Daraktan CISLAC, Kwamared Auwal Ibrahim Musa Rafsanjani ya ce, a cikin shekaru 20 da suka gabata, CISLAC/TI-Nigeria tana aiki da hukumomin zartarwa, majalisun dokoki, kungiyoyin Jama’a, Al’umma da kafafen yada labarai a jihar Kano, musamman a bangaren kula da lafiyar mata da kananan yara, kiwon lafiyar yara da Iyali, kula da yara da tattalin arziki, samar da Rigakafin Farko, wayar da kan al’umma kan tsare-tsare don ci gaba.
Mun yaba da kokarin da hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC) ke yi wajen tabbatar da gaskiya da rikon amana a jihar domin samar da kyakkyawan shugabanci da tabbatar da samar da ingantacciyar hidima ga al’ummar jihar, CISLAC ta amince da Kano a matsayin jiha mai dabara a cikin ayyukanmu,” inji Rafsanjani.
Ya yaba da dimbin nasarorin da hukumar ta samu a karkashin jagorancin Barr. Muhuyi Magaji Rimingado, duk da kalubale daban-daban na hana yaki da cin hanci da rashawa da suka hada da samar da ingantaccen tsari, dabarun yaki da cin hanci da rashawa na jihar Kano da samar da cikakken tsarin aiki ga ma’aikatun gwamnati tare da kafa ofisoshi a dukkanin kananan hukumomi 44 na jihar.
A nasa bangaren, korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa na jihar Kano, Barr Muhuyi Magaji Rimingado, ya yaba da goyon baya da hadin gwiwar da babban darakta na CISLAC, Auwal Ibrahim Musa Rafsanjani ke ba shi, wanda a kodayaushe ya kasance tare da hukumar wajen yaki da cin hanci da rashawa ta fuskar kalubale da dama.
A cewar shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, duk da dimbin kalubalen da hukumar ke fuskanta, hukumar ta samu nasarori ta yadda baya ga yaki da cin hanci da rashawa a dukkan matakai a jihar, aikin da ya rataya a wuyanta a matsayin mai kula da almundahana ya taimaka wajen warware matsaloli da dama cikin ruwan sanyi.