Zabe kan gyaran kundin tsarin mulki ta Intanet: Gbajabiamila ya yi barazanar bayyana sunayen ‘yan majalisar da ba su halarta ba

Femi Gbajabiamila 1
Femi Gbajabiamila 1

Shugaban Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila, ya yi barazanar buga sunayen ‘yan majalisar da ba su halarci zaman majalisar ba a lokacin zabe na gyaran kundin tsarin mulkin wanda za’a yi a ranakun 2 da 3 ga Maris.

Gbajabiamila, wanda ya bayyana hakan a zaman majalisar a ranar Laraba, ya bukaci ‘yan majalisar da su shiga zaben saboda muhimmancinsa ga ci gaban kasa kasa.

“Mambobin majalisa, za mu kada kuri’a kan gyaran kundin tsarin mulki na farko a ranakun 3 da 4 ga Maris.

“Yana da mahimmanci cewa dukkan membobin su kasance a ranakun Laraba da Alhamis, za mu buga sunayen duk wanda basu halarta ba,” in ji shi.

Shugaban majalisar ya ce babu wani dan majalisa da za a ba shi damar gudanar da aikin sa ido ko na kwamitin a cikin kwanaki biyun da aka kebe domin gyara.

Ya ce ana sa ran kowane memba zai kasance a kasa domin kada kuri’arsa, inda ya ce ba za a yi taron komitoci da sa ido ba.

A wani labarin kuma, Uwargidan shugaban kasa, Uwargida Aisha Buhari ta je zauren majalisar wakilai a safiyar yau domin nuna goyon bayanta ga matan kan batun sake duba kundin tsarin mulkin kasar.

Gbajabiamila ya ce uwargidan shugaban kasar ta kasance a zauren majalisar domin nuna goyon bayanta ga matan kan gyaran kundin tsarin mulkin kasar.

Ya ce ta zo ne domin ta ba da goyon baya ga matan.

Gbajabiamila ya kara da cewa ‘yan majalisar ba su damu da nauyin ofishinta na inganta rayuwar mata ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here