Hukumar NYSC ta sanar da sabuwar ranar da za ta fara biyan alawus na Naira dubu 77

NYSC NYSC 750x430

Babban darakta janar na jukumar kula da yi wa masu kasa hidima (NYSC) Birgediya Janar Olakunle Nafiu, ya tabbatar wa mambobin hukumar cewa za a fara aiwatar da sabon alawus alawus na Naira 77,000 duk wata daga watan Maris na 2025.

Shugaban hukumar ya bayar da wannan tabbacin ne a lokacin wata tattaunawa da masu yi wa kasa hidima a ofishin shiyya ta NYSC na Wuse da Garki da ke Abuja, yayin da ya jaddada kudirin hukumar NYSC da gwamnatin tarayya na ci gaba da kyautata rayuwar su.

Wannan ci gaban ya zo ne watanni bayan hukumar NYSC ta bayyana shirin kara alawus din daga Naira dubu 33 zuwa Naira 77 daidai da sabon mafi karancin albashi na Naira dubu 70 da Shugaba Bola Tinubu ya amince da shi a watan Yulin 2024, bayan karin da aka samu a baya a shekarar 2019 zuwa Naira dubu 33, shi ma ya biyo bayan bitar mafi karancin albashin Naira dubu 30.

A cikin sanarwar da mukaddashin daraktar yada labarai da hulda da jama’a, Caroline Embu, ta sanya wa hannu, NYSC ta ce amincewar N77,000 na kunshe ne a cikin wata takarda daga hukumar kula da ma’aikata ta Albashi da kudaden shiga da ma’aikata, mai kwanan wata 25 ga Satumba 2024 kuma shugaban hukumar Ekpo Nta, ya sanya wa hannu, daidai da dokar da ta kafa dokar karancin albashi ta kasa.

Karin karatu: Majalisar Wakilai ta amince da ayyana dokar ta-ɓaci a Rivers

Birgediya-Janar Nafiu ya jaddada cewa jin dadin masu yiwa ƙasa hidima ya kasance babban abin da ya sa a gaba, don haka ya bukace su da su kasance masu natsuwa, sadaukar da kai, mai da hankali da kuma da’a wajen yi wa kasa hidima.

Ya kuma yaba da hangen nesan iyayen da suka kafa NYSC, inda ya bayyana shirin a matsayin wata muhimmiyar cibiya da ke samar da hadin kan kasa ta hanyar fallasa daliban da suka kammala karatunsu ga al’adu daban-daban a fadin Najeriya.

Ya kuma tabbata ds cewa masu yi wa kasa hidima na NYSC za su ci gaba da sanya dabi’u kamar kishin kasa, da’a, shugabanci, da hada kai a kowane sabon rukuni.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here