Babbar kotun jihar Rivers da ke zamanta a Port Harcourt ta hana babban alƙalin jihar, Mai Shari’a Simeon Chibuzor Amadi, karɓa ko aiwatar da kowace takarda daga majalisar dokokin jihar Rivers da ta shafi yunƙurin tsige gwamnan jihar, Siminalayi Fubara, da mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Nma Odu.
Umarnin ya fito ne daga babbar kotun Oyibo da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Oyibo, bayan shigar da ƙara biyu daban-daban da gwamna da mataimakiyarsa suka gabatar, masu lambobin shari’a OYHC/7/CS/2026 da OYHC/6/CS/2026.
A cikin umarnin wucin-gadi na hana aiwatarwa, kotun ta hana kakakin majalisar dokokin jihar Rivers, Martin Amaewhule, da wasu mutum 32, ciki har da sakataren majalisar da babban alƙalin jiha, ɗaukar kowanne mataki da ya shafi tsarin tsige gwamna.
Kotun ta fayyace cewa Mai Shari’a Amadi ba zai karɓa, tura, nazarta ko aiwatar da kowace buƙata, ƙuduri, takardun tsige shugabanci ko wata hanyar sadarwa daga waɗanda ake ƙara na farko zuwa na 27 ba, domin kafa kwamitin bincike kan zargin rashin da’a da ake yi wa gwamna da mataimakiyarsa, na tsawon kwanaki bakwai.
Mai Shari’a F. A. Fiberesima, wanda ya jagoranci shari’ar, ya bayar da wannan hukunci ne yayin amincewa da buƙatun gaggawa da gwamna da mataimakiyarsa suka gabatar a shari’o’in biyu.
Karin labari: Rikicin jihar Rivers: Ƙarin ƴan majalisa biyu sun janye daga yunkurin tsige Fubara
Kotun ta kuma ba da izinin miƙa umarnin wucin-gadi da takardun fara shari’a ga waɗanda ake ƙara na farko zuwa na 31 ta hanyar manna su a ƙofar gidajen majalisar dokokin jihar Rivers.
Haka kuma, kotun ta umurci a miƙa umarnin wucin-gadi da takardun shari’a ga wanda ake ƙara na 32, wato babban alƙalin jihar Rivers, ta hannun kowane ma’aikacin shari’a a ofishin babban alƙalin da ke cikin harabar babbar kotu, tare da ɗage shari’ar zuwa wani lokaci domin sauraron ƙarar da aka sanar.













































