Kotun Koli Ta Umarci INEC Ta Maye Gurbin Shekarau da Hanga a Matsayin Dan Takarar Sanatan Kano ta tsakiya a NNPP

Rufai Sani Hanga
Rufai Sani Hanga

Kotun koli ta tabbatar da Sanata Rufai Hanga a matsayin sahihin dan takarar sanatan jam’iyyar NNPP a Kano ta tsakiya, a zaben ‘yan majalisun tarayya da aka yi a ranar 25 ga watan Faburairu.

Wannan na zuwa ne a hukuncin da kotun ta yanke a zamanta da alkalai biyar karkashin jagorancin mai shari’a Inyang Okoro a ranar Juma’a 10 ga watan Maris.

Kotun ta ce hukumar zabe ta INEC ta yi kuskuren rashin maye gurbin Sanata Ibrahim Shekarau da Hanga bayan da Shekarau ya yi hijira zuwa jam’iyyar PDP.

Mai shari’a Emmanuel Agim a takardar hukuncin da ya karanta wacce mai shari’a Uwani Abba-Aji ta rubuta ta yi watsi da abin da INEC ta gabatar a baya.

Kotun ta tabbatar da hukunci biyu da babban kotun tarayya da ta daukaka kara da ke Abuja suka yanke na tabbatar da Hanga a matsayin dan takarar NNPP.

Karin bayani na nan tafe…

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here