Taliban ta kama wani da ake zargin ya yi uwa da ‘yarta fyaɗe

wp content uploads 2020 08 Police arrest man for Sodomy
wp content uploads 2020 08 Police arrest man for Sodomy

Taliban ta tabbatar da kama wani da ake zargin ya yi wa wata mata da ‘yarta ‘yar shekara 12 a kauyen Khanqah da ke lardin Sarpul fyaɗe.

A cewar rahotanni da bayanan da matar ta bayar, ta ce a yammacin ranar 9 ga watan Maris, lokacin da mijinta ya fita wajen aiki, wasu ’yan Taliban biyu sun shiga gidansu da sunan bincike bayan sun rufe musu hannaye, sannan suka ƙeta musu haddi.

An ce waɗannan mutane biyu sun bar gidan lokacin da yanayi ya ragu, inda makwaɓta suka ɗauki yarinyar zuwa asibiti bayan da ta yi ta zubar da jini.

Mako guda da bayar da rahoton faruwar lamarin, jami’in yaɗa labarai na ‘yan sandan Samangan, ya tabbatar da aikata fyaɗen, ya kuma ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan waɗannan mutane, amma bai bayyana waɗanda ake tuhuma ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here