Kimanin yara 60 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar sankarau a kananan hukumomin Gwandu, Jega da Aliero na jihar Kebbi, yayin da cutar ke yaduwa cikin sauri a yankin Arewa maso yammacin Najeriya, musamman a jihohin Kebbi da Sokoto.
Tuni dai kungiyar likitocin da ba ta da iyaka (MSF), wacce aka fi sani da Doctors Without Borders, ta yi gargadi.
Kungiyar likitocin agaji ta ce ana bukatar daukar matakan gaggawa don dakile barkewar cutar sankarau, wadda tuni ta kama sama da mutane 500 a Gwandu, Jega da Aliero.
Dr Galtimari ya ce an tura kungiyoyin likitocin don kula da marasa lafiya, samar da asibitoci da magunguna masu mahimmanci, da horar da ma’aikatan kiwon lafiya.
Ya kara da cewa, a Sokoto da ke makwabtaka da Kebbi, kungiyar na kara zage damtse wajen gano masu kamuwa da cutar yayin da suke shirye-shiryen gudanar da babban gangamin rigakafin tare da jami’an lafiya na jihar.
Karin karatu: Hukumar Nimet ta yi gargaɗi kan ɓullar cutar sanƙarau a Najeriya
Cutar sankarau, wacce kwayoyin cutar Neisseria meningitidis ke haifarwa, wanda ka iya haifar da mutuwa idan ba a kula da su ba, inda aka kiyasta kashi 80 cikin 100 na mace-mace a lokuta masu tsanani.
Alamomin sun hada da zazzabi mai zafi, taurin wuya, ciwon kai mai tsanani, amai, da kamewa.
MSF ta bukaci hukumomi da su hanzarta kokarin yin rigakafin, tana mai gargadin cewa jinkiri na iya haifar da karin mace-mace da za a iya rigakafinta.