Dakarun Djibouti sun fice daga tsakiyar Somaliya saboda rikicin cikin gida

Djibouti, dakarun, Somaliya, fice, rikicin
A ranar Talata ne dakarun ƙasar Djibouti da ke aiki ƙarkashin rundunar wanzar da zaman lafiya ta Tarayyar Afirka a Somaliya (Atmis) suka fice daga wani...

A ranar Talata ne dakarun ƙasar Djibouti da ke aiki ƙarkashin rundunar wanzar da zaman lafiya ta Tarayyar Afirka a Somaliya (Atmis) suka fice daga wani babban sansanin soji da ke tsakiyar garin Beledweyne a yankin Hiiraan saboda kasancewar dakarun yankin da ke gaba da juna.

Sama da shekaru 10 ne sojojin ke jibge a garin kafin janyewar.

Karin labari: “Yadda na sulale daga hannun ‘ƴan fashin daji” – Ɗalibi

Rahotanni sun ce dakarun yankin na da rikicin siyasa ne kasancewar daya sansani mai goyon bayan gwamnatin yankin na Hirshabelle ne yayin da daya kuma ke da alaka da bangaren ‘yan adawa masu ɗauke da makamai da aka fi sani da jihar Hiiraan.

Gwamnatin tarayyar Somaliya da jami’an na Hiiraan ba su ce komai ba game da janyewar.

Karin labari: Da Dumi-dumi: Majalisar dattawa ta dakatar da Abdul Ningi

Rahotanni sun ce sojojin Djibouti sun fice daga sansanoninsu ne bayan tattaunawa tsakanin shugaban Atmis Souf Mohamed El-Amine da mataimakin wakilin Majalisar Dinkin Duniya Raisedon Zenenga.

Janyewar na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar al-Shabab ta kwace wasu yankuna a jihar Galmudug mai makwabtaka da ita, inda sojojin gwamnatin Somaliya suka yi watsi da sansanoni da dama.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here