Zan Yi Amfani Da Rahotannin Zargin Cin Hanci Da Rashawa Wajen Zabar Ministocina, Ganduje Da Wasu Ka Iya…

0

Ganduje and Tinubu

Mai yiwuwa tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, da wasu jiga-jigan jam’iyyar APC mai mulki ka iya gaza samun gurbin ministoci kamar yadda rahotanni suka ce shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya shirya amfani da zarge-zargen tsaro da cin hanci da rashawa wajen yanke hukunci kan ministocinsa.

Tinubu wanda aka rantsar a ranar 29 ga Mayu, 2023, yana da kwanaki 60 na gabatar da ministocinsa kamar yadda dokar da aka yi wa kwaskwarima ta tanada.

Shugaban kasa a yunkurinsa na cika wa’adin ne a yau (Lahadi) ya cika kwanaki 48 da hawansa mulki, tuni ya aika da wasu sunaye ga hukumomin tsaro domin tantancewa gabanin mika sunayen ministoci ga majalisar dattawa kafin ranar Alhamis 27 ga watan Yuli. 2023.

A ranar 27 ga watan Yuli ne ‘yan majalisar dattawa za su tafi dogon hutu, amma rashin gabatar da sunayen ministocin na iya jinkirta hutun nasu.

Rahotanni sun tabbatar cewa shugaban kasar ya mika sunayen wasu mutane ga hukumomin tsaro domin tantancewa, sai dai wasu majiyoyi masu karfi sun ce bayanan nasu ba wata alama ce da za su iya sanya sunayen wadanda aka nada a karshe an gabatar da su ga majalisar dattawa domin tantance su ba.

Wata majiya tace, Shugaban kasar maimakon kin amincewa da shi, zai yi amfani da rahotannin don duba wanda zai nada ministoci.

Rahotanni sun ce tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umaru Ganduje wanda ya tare a fadar shugaban kasa tun bayan da ya kammala wa’adin mulkin sa a matsayin gwamna na iya kasancewa cikin wadanda za a gaza amincewa da nadinsa saboda zarginsa na cin hancin bidiyon dala da Kano ke bincike a halin yanzu.

Hakazalika, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle shi ma za a iya fitar da shi bisa zargin damfarar N70bn da EFCC ta yi masa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here