Gwamnatin jihar Kano ta fara kwashe tarkacen shara a kan manyan tituna a cikin birnin bayan fitar rahoton Solacebase.
Jaridar SOLACEBASE ta ba da rahoton a ranar Asabar yadda tulin shara ya mamaye manyan tituna a cikin birni duk da haɗarin lafiya da ke tattare da shi.
Sai dai a ranar Lahadi, kwamishinan muhalli na jihar, Hon. Nasiru Sule Garo ya umurci hukumar kula da tsaftar muhalli ta jihar Kano da ta gaggauta daukar mataki tare da kwashe sharar.
Lokacin da Jaridar Solacebase ta ziyarci kasuwar Yan Kura ta gadar sama, a ranar Lahadi, an ga tawagar maaikata dake kwashewa suna gudanar da aikin.
An kwashe fiye da tireloli goma na sharar gidaje yayin aikin wanda aka gudanar da misalin karfe 1:00 na ranar Lahadi.
Da yake zantawa da jaridar Solacebase kan wannan ci gaban, Nasiru Sule Garo ya ce rahoton ya kasance kalubale ga gwamnati wajen kara kaimi don kwashe sharar gidaje da kuma sarrafa shara a jihar.
Garo ya alakanta tsarin kula da sharar gida mai wahala a jihar da abin da ya gada daga gwamnatin da ta shude da ta soke hukumar kula da tsaftar muhalli ta jihar Kano (REMASAB) tare da bai wa wani kamfani mai zaman kansa kula da sharar gidaje.
Idan za a iya tunawa cewa an soke hukumar REMASAB a watan Yunin 2021 lokacin da gwamnatin jihar ta rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniya ta fahimtar juna (MoU) tare da wani kamfani mai zaman kansa, Capegate Investment Company Limited, domin aikin kwashe sharar gidaje da sarrafa ingancin iska.













































