Sabbin rikice-rikice sun sake aukuwa a Ƙaramar Hukumar Riyom ta Jihar Plateau a daren Lahadi, inda wasu ‘yan bindiga suka kai hare-hare a kauyen Jol da Dorowa Babuje (gundumar Rob), tare da kashe aƙalla mutum 10 tsakanin ƙarfe 8:00 na dare zuwa 9:00 na dare, kamar yadda shugabannin yankin suka tabbatar.
Shugaban Ƙungiyar Matasan Berom ta ƙasa (BYMA), Barrista Solomon Dalyop, ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa ta wayar tarho da wakilin gidan talabijin na Channels a Jos.
Ya ce an kashe mutum tara a Dorowa Babuje, yayin da mutum guda ya rasa ransa a Jol a hare-haren da suka faru kusan lokaci guda amma a wurare daban-daban.
A cewarsa, maharan da suka kai hari a Jol sun iso ne a kan babura daga yankin Manga, duk da cewa tun da wuri aka sanar da hukumomin tsaro kan yiwuwar motsin wasu mutane a yankin.
Ya bayyana cewa jami’an Operation Rainbow, rundunar tsaron Jihar Plateau, sun riga sun isa wurin kuma sun samu nasarar fatattakar maharan, lamarin da ya takaita yawan asarar rayuka.
A Dorowa Babuje kuwa, Dalyop ya ce maharan sun fito ne daga yankin Jong-Wereh, inda ake zargin sun jima suna sansani. Ya kara da cewa an sanar da sojoji cikin gaggawa kuma sun mayar da martani cikin sauri, abin da ya hana adadin mutanen da suka mutu ƙaruwa.
Yunkurin jin ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar bai yi nasara ba, domin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan Plateau, Alfred Alabo, bai amsa kiran waya ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Har yanzu rundunar ‘yan sandan Najeriya ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan hare-haren ba.
Wannan sabon kisan ya kara nuna yadda hare-hare ke ci gaba da maimaituwa a Riyom, daya daga cikin yankunan da rikice-rikice suka fi kamari a Jihar Plateau, inda al’ummomin manoma ke fuskantar hare-haren dare, kwanton bauna da kaura daga muhallansu a ‘yan watannin nan.
Mazauna Jol da Dorowa Babuje sun shiga cikin fargaba, yayin da iyalai ke jimamin wadanda suka rasa, tare da kira ga a samar da cikakken tsaro na dindindin domin hana sake zubar da jini.
A halin yanzu, kungiyoyin matasa da shugabannin al’umma sun sake kira ga gwamnatocin tarayya da ta jiha da su dauki matakan tsaro da samar da zaman lafiya na dogon lokaci a Riyom da sauran al’ummomin makwabta.













































