Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dage sauraron karar neman kare hakkokin dan Adam da wanda ake zargi da shiga tsakani a tattaunawar ‘yan ta’adda, Malam Tukur Mamu, ya shigar kan Babban Lauyan Tarayya (AGF), zuwa ranar 23 ga Afrilu domin karbar takaitattun bayanan karshe na rubuce daga bangarorin biyu.
Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa (NAN) ya ruwaito cewa Mamu na kalubalantar ayyana shi a matsayin “dan ta’adda” da AGF ya yi, alhali yana fuskantar shari’a a kotu.
An shirya karbar takaitattun bayanan ne a gaban Mai Shari’a Mohammed Umar, amma ba a samu ci gaba ba, inda kotun ta sake sanya ranar 23 ga Afrilu domin ci gaba da shari’ar.
Tun a ranar 25 ga Nuwamba, 2025, lauyan Mamu, Johnson Usman, SAN, ya shaida wa kotun cewa matakin da AGF ya dauka ya saba da Sashe na 36(5) na Kundin Tsarin Mulkin 1999, wanda ya tanadi cewa ana daukar wanda ake tuhuma a matsayin mara laifi har sai kotu ta tabbatar da laifinsa.
Usman ya ce sun hada kwafin rahotannin da kafafen yada labarai suka wallafa inda aka ayyana wanda yake karewa a matsayin dan ta’adda a matsayin hujjoji a cikin karar.
Babban lauyan ya roki kotun ta amince da bukatunsu ta hanyar kare hakkokin Mamu.
A cikin karar mai lamba FHC/ABJ/CS/713/2024, Mamu ne mai kara, yayin da AGF shi ne kadai wanda ake kara.
Usman ya ce duk da cewa Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da wanda yake karewa kan zargin laifukan ta’addanci, ba daidai ba ne ta ayyana shi a matsayin dan ta’adda a yayin da shari’ar ke gudana.
Ya ce sun rubuta wa AGF suna neman a janye ayyana shi a matsayin dan ta’adda, amma ba a amsa musu ba.
Ya kara da cewa takardar martani da Gwamnatin Tarayya ta shigar kan karar na nuna amincewa da zargin da ake yi.
Usman ya jaddada cewa ta fuskar doka, dabi’a da addini ba daidai ba ne a ayyana Mamu a matsayin dan ta’adda alhali ba a same shi da laifi ba.
“Ita ce kotu kadai ke da ikon ayyana mutum a matsayin dan ta’adda bayan an same shi da laifi kuma an yanke masa hukunci.
“Mai shari’a ne kadai ke da wannan iko da hakki, ba wanda ake kara ba a wannan shari’a.
Sai dai lauyan AGF, David Kaswe, ya yi watsi da hujjojin Usman.
Ya ce sun shigar da takardar rantsuwa mai sakin layi biyar a matsayin martani ga karar.
Ya ce batun da ke gaban kotu shi ne ko AGF na da ikon ayyana wanda ake tuhuma a matsayin dan ta’adda a lokacin da aka yi hakan.
A cewarsa, dokar ta yi daidai da Sashe na 36 (1 zuwa 12) na Kundin Tsarin Mulki da kuma Sashe na 49 da 50 na Dokar Yaki da Ta’addanci ta 2022.
Ya ce wadannan tanade-tanade sun bai wa AGF ikon ayyana kowa a matsayin dan ta’adda.
Da yake ambato Sashe na 49 na dokar, ya ce idan Kwamitin Takunkumi ya samu dalilai masu karfi na zargin cewa mutum ya aikata ko ya yi kokarin aikata ta’addanci, ko ya taimaka ko ya dauki nauyin ta’addanci, ko yana aiki a madadin wani, kwamitin na iya ba AGF shawarar a ayyana shi a matsayin dan ta’adda.
Mai Shari’a Umar ya tambayi lauyan AGF ko ya dace a ayyana wanda ke fuskantar shari’a a matsayin dan ta’adda kafin a kammala shari’ar.
Kaswe ya dage cewa an yi hakan ne bisa doka.
Mai shari’ar ya tambaye shi abin da zai faru idan a karshe kotu ta wanke shi daga zargin ta’addanci.
Kaswe ya amsa cewa dokar ta bai wa Kwamitin Takunkumi, wanda ke zama duk bayan watanni uku, ikon sake duba ayyanawar.
Ya roki kotu ta yi nazari sosai kan Dokar Yaki da Ta’addanci tare da kwatanta ta da Sashe na 36 na Kundin Tsarin Mulki.
Ya roki kotu ta yi watsi da dukkan bukatun da Mamu ya gabatar, tare da tabbatar da cewa AGF na da ikon ayyana shi a matsayin dan ta’adda bisa doka.
Sai dai Usman ya ce dogaro da Sashe na 49 na Dokar Yaki da Ta’addanci ya ci karo da Sashe na 36 na Kundin Tsarin Mulki.
Ya ce an shigar da karar ta’addanci kan Mamu ne a 2023, amma an ayyana shi a matsayin dan ta’adda a 2024.
A cewarsa, da an yi ayyanawar kafin a gurfanar da shi a kotu da ya dace, amma bayan an gurfanar da shi kuma ana karbar shaidu, sai a sake ayyana shi a matsayin dan ta’adda.
“Bisa tanadin Sashe na 36(5) na Kundin Tsarin Mulki, ana daukarsa a matsayin mara laifi har sai an same shi da laifi.
“Dogaro da Sashe na 49 na dokar domin hukunta wanda ke fuskantar shari’a ya saba doka kuma ya kamata a soke shi,” in ji Usman.
Mai Shari’a Umar ya bukaci karin bayani musamman kan Sashe na 36 na Kundin Tsarin Mulki da Sashe na 49 na Dokar Yaki da Ta’addanci.
Daga nan kotun ta dage shari’ar zuwa ranar 23 ga Fabrairu, 2026, domin karbar takaitattun bayanan karshe na bangarorin biyu dangane da wadannan tanade-tanade.













































